Thursday, July 30, 2020

Wa Zai Furta? Page 30 Karahe - ZAZZAFA TV



30 July 2020

🀐 *WA ZAI FURTA?*🀐
              30

*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri'a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.*


*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*

*Domin ki...... beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*

πŸ‘‰πŸΌπŸ’žπŸ’•πŸ’•  *MOM SAUDA AND SALMA I love you so much, remember this always*πŸ₯°πŸ˜πŸ˜˜.

*NA SADAUKAR DA LABARIN WA ZAI FURTA GA DUKKAN FANS DINA MASU SON LABARIN WADANDA KE GROUPS DA WADANDA BASA CIKI AMMA SUNA KARANTAWA*

    ******************
*KANO NIGERIA*
....... Ya dan yamutsa fuska ya rike hannunta suka Fara tafiya a hankali, yana Jin yanda hannun nata ke karkarwa tana kyarma.
  ..... Suna hawa step daya , biyu ya runtse ido ya saketa da sauri ya duka tare da dafe ciki .....Bilkisu cikina.
  Ta zaro ido da sauri cikin tsoro saboda tun a party taga yanayin sa duk ya canza, ta Dan duka itama tana leken sa cikin ke ciwo?
Ya daga Mata Kai da kyar.... Innalillahi ta fada tare da kamoshi suka Mike...... Tafiya sukeyi da kyar da kyar, ya Dan kalleta Ina Jin yunwa ce Bilkisu rabona da abinci tun jiya da safe...... Subhanallah ta fada a hankali.
........... Katon daki ne yasha kayan alatu, makeken gado da wordrop ga wasu irin kujeru a gefe babu tarkace a dakin amma ya tsaru da kayan kece raini.
   Ga mamakin ta an jera kayan ciye cite bisa kafet din.....ya tafi luuuuu ta Kara taro Shi tare da fadin *Na shiga uku* da karfi.
Suka Fadi rikichaaa bisa carpet din saboda Bata da karfi ko kadan...... Ya riketa gammm idanun sa rufe *Bilkisu cikina*.... ..Anwar ko dai a Kira sadeeq muje asibiti.... Kiban abincin sa naci Dan Allah ya nuna wurin da hannu.
Da sauri ta janyo dan table din da suke sama.... Ya Kara dafe ciki Fara bani something liquid please...... Ta dauko robar fresh milk Mai sanyi ta Mika mishi ya kafa Kai ya shanye, ta bude wani glass bowl sai ga dambun naman kaji ta Mika mishi ga dambu kaci....na koshi. Ta zaro ido Dan Allah kaci Anwar tunda har ka gano matsalar ka yunwa ce... Bazan ci ba ya fada da sauri..... Saboda me?
Saboda ke bakici ba .... Zanci kaci tukun...... Bazan ci ba sai kinci.
Zata Kara magana ya ce Miko madarar, ta Miko da sauri tunanin ta sai Kara ne, ya ce okay shanye duka sai ki ban naman.
Tayi shiruuuu, ya Dan kalleta mayar idan bakyaci duk mayar dasu...... A'a Zan sha ta kafa Kai..... Itama kusan abincin rabonta dashi tun jiyan.
  Tana ajiyewa ya tura Mata naman ci sannan yasha mur Yana yamutsa fuska...... Tayi shiruuuu...... Kawai ya Mike da gudu yayi toilet ta jiyo Yana kakarin amai.... Hankalin ta ya tashi matuka lallai Anwar baya lafiya ta mike tsaye ta kura ma kofar ido...

 Ya fito Yana layi ta karasa da sauri ta rikoshi sannu ko dai za a je hospital Anwar??...... Matsalata yunwa ce Dana ci shikenan kinsan ni bana wasa da abinci.... Na sani ta fada tana kamashi lokacin da zai zauna.... Ta tura mishi naman kaci Dan Allah ....... Wallahi bazan ci ba sai kinci ke meye Kika ci?
Meye acikin can?
Ya nuna cooler ta janyo da sauri ta bude..... PeppΓ© soup ne okay zuban acan, ya nuna plate..ya dafe ciki tare da dukewa Yana matse ido.
Ta dauko duk ta gigice ta zuba tana gamawa har lokacin bai dago ba, ya ce maza shanye ki zuban nawa a ciki...
    Ba yarda ta iya saboda tasan Anwar da kafiya, itama yunwar duk ta addabeta ba yanda ta iya ne, Dole ta dage sai gashi ta shanye tas!, Ta zuba mishi ta mika mishi, ya dan kalleta ya ce kafin na gama kici dambun nima Ina son cin sa.... Shima ta janyo ta Fara tsakura........ Haka haka sai ga Bilkisu tayi Nat! Hada uwar gyatsa.
  Shi kuwa Wanda ta zuban ya turo ya ce bai iyaci ya kwanta Yana murkususu....... Ta karaso da sauru kamar zatayi kuka .....Anwar ko dai muje asibiti.... Karki damu da nayi barci shikenan.... Ya Dan gyara ya kwanta ruf da ciki ya juya kawai.
Ta zabga tagumi kawai sai Kuma ta Fara kwallah. Yana jinta tana ta sharbe..... A hankali taji Yana saukar numfashi alamar yayi barci, ta Kura mishi ido.... A hankali barci ke neman daukarta itama, ta Fara gyangyandi....... Barawo Bata San ya sace ta ba .... Yana kwance yaji alamar hannunta.... Ya Dan juyo sai kawai yaga ta yi barci....... Ya danyi dariya ya tashi zaune...... Duk plan ne yayi don baisan ta Ina zai tarbo rigimarta ba.
  Ya janye kayan ya koma gefe ya zuba ya cika cikin sa ya cire kayan say ya watso ruwa ... Yayi tsaye kanta Yana zullumin Allah yasa idan ya tabata kada ta tashi.
Sai da ya tabbatar ya gama komai ya kashe fitila sannan ya zukunna ya sungumeta a hankali a jiye bisa gado, ta saki ajiyar zuciya tare da gyara kwanciya barcin ya riga ya dauketa.....ya rage sanyin A.C saboda dakin yayi sanyi da yawa ya Kai hannu a hankali ya Fara cire mata jewelries dinta ..... Yaci gaba da zuge zip......... A firgice ta bude ido.....amma Ina is too late to cry... Zata kurma mishi ihu ya yi saurin rufe bakin da nasa..... Ta rasa inda zata sa kanta....ya riga ya cimmata.... Wasu zafafan hawaye kawai ke fita..............
Ya saki ajiyar zuciya a hankali ya Kara rungumeta a kirji ya lumshe ido ya kasa magana baya iya cewa komai..... Tayi tayi ta tureshi ta kasa ya riketa gammm. Ta Kara sakin kuka ta sunne Kai jikinsa, duk jikin ta yayi tsami....... Yaja blanket ya rufe su..... Ajiyar zuciya kawai takeyi Shi kuwa ya rasa abin yi duk ya gama kidimewa ya kasa kwakkwaran motsi..... Zuwa can yaji ta Fara sakin numfashi a hankali alamar tayi barci....ya Kara mannata jikinsa kirjinsa na harbawa a hankali..... Shikam cikin kunnensa aka Kira sallah..... Ya zame a hankali ya fada toilet.
  Kasa zuwa masallaci yayi. Ya saka jallabiya Mai karamin hannu ya feffesa turaruka ya shiga wani daki ya fito da doguwar Riga, pant, bra da under skirt ya ajiye Mata bisa abun sallah..... ya koma gadon ya shige bargo ya Kara janyota jikinsa......
  Barci Mai nauyi yayi awon gaba dashi.
  Tafi mintuna goma da farkawa..... Tayi shiruuuu ta tabbatar da lallai barci yakeyi ta zame jikinta a hankali ta sauka gadon, tayi toilet da sauri.....  Tana shiga ta zukunna ta Kara sakin kuka.... Sai da tayi Mai isarta sannan ta fada cikin kwami.
  Ba wani extra towel Dole Wanda yayi amfani dashi ta daura.
Ta leko a hankali har lokacin barci yakeyi ta sadado ta dauki kayan da ta hango ta koma da sauri....
A toilet din ta shirya, ta fito. Tana cikin yin sallah ya farka...... Lokacin da ta sallame taji motsinsa sai kawai ta koma tayi sujada Bata Kara dagowa ba.......  Ya kyalkyace da dariya ya taso.
Tana Jin Yana yowa inda take sai kawai ta Fara kuka......
Ya sungumeta yayi bisa gado Yana fadin ai na Sami Baki yanzu Zan bada hakuri wannan laifi Dana tabka....... Ta sunne Kai.
Ya dagota Bilkisu Allah yayi Miki albarka ya sa daddy da mommy aljannah firdausi... Hakika sun Baki tarbiyya Mai kyau a rayuwa.
Ya rungumeta kiyi hakuri wannan Shi ake Kira *Aure* Kuma wannan kadai zai tabbatar Miki da *how much I love you* kinji ko?
 Ta yi shiru.....
Lafiyata Lau jiya Yar dabara nayi ki Samu kici abinci saboda na tabbatar bana iya kyaleki jiya Kam .....
Zo muje ya figi hannunta...... Tafiya sukeyi bayan gidan suka zagaya can...... Sai gasu sashen Hajiya.... Tayi saurin janye hannunta... Yayi dariya kunya kikeji?
Idan Kika ringa wannan sum sum din Zaki to nawa kanki asiri ace jiya..... Ta Kai mishi duka dai dai hajiyar na fitowa.... Ya buga tsalle Yana dariya... Hajiya ta washe Baki...... Bilkisu mijin ake duka?
Ta kusa Suma don kunya ta zukunna da sauri ta ce *Ina kwana*
  Ta yi Yar dariya lafiya Lau kuxo ga break din can......
Sai kusan azahar suka bar sashen ta dan sake kadan....
Suna shiga ya rikota zo ki gani..... Yabi da ita wani corridor suka shiga wani falo ya ce nan ma naki ne fa, ya bude bedroom din sai ga wasu irin set na gado royal masu kyau gefe jakun Kuna ne set talatin da shidda ya ce ga lefen ki Zaki gani Yanzu ko ba Yanzu ba?
Ta sunne Kai jikin sa kawai.... Ya danyi dariya *Bilkisu kunya*...............
 Ya kamota ya zauna a kujera ita Kuma tana bisa cinyarsa.
Gaskiya kin saka ni farinciki Bilkisu naji dadi jiya har mutuwa nayi na dawo..... Bata San lokacin da ta kyalkyace da dariya ba .... Shima ya Kama dariyar ya ce Allah kinji nayi magana? Ai kasawa nayi.
... Next week zamu tafi Dubai a can zamu zauna Ina da gida a can, sadeeq zai ringa taking care na business din Nigeria tare da taimakon su Suleiman...... Ni Kuma Zan ci gaba da duba na sauran countries din nida su Alhaji murtala..... Kina son Zama Dubai?
Ta danyi murmushi ta ce um.Daga nan Zaki dauki Yan aiki ko kina son na can?
Duk yanda ka gani.... Yayi murmushi.
Zan baki appointment idan result ya fito kema kina amsar albashi kin San hausawa na cewa *Da namu gwamma da nawa* ya karasa maganar Yana dariya.... Kin San duk wakokin bikin Nan nafi son wakokin da *Aliyu nata* yayi Mana?
Ta danyi dariya gaskiya ya iya Waka, ya ce sosai ga babu zagi, ba habaici babu maganar banza yaron ya zo da basira Mai tsafta Shi yasa ake rububinsa..........
Ya Dan taba cikin ta Allah yasa jiya Yara sun shiga...... Ta soke Kai jikinsa..... Ya kyalkyace da dariya.............✍🏼

    *KARSHE*

Allah ya bada zaman lafiya da zuri'a dayyiba.
Muna rokon Allah ya karemu daga cututtukan zamani.
  Abinda muka karanta Allah yasa mu amfana da lesson din ciki na Shi mutunci Riga ne, ya kamata mu sani kunya na daya daga cikin abinda ke daga darajar mace a duk inda take.
Kwadayi baya Kai mutum ko Ina sai tushen wulakanci da Kuma nadama.
    Mai kudi da talaka duk bayin Allah ne, masu kuci da ke nuna Basu iya rayuwa tare da talakawa ku sani rayuwar dasu bazai rage ku da komai ba sai dai na ku Kara samun daukaka, mutuncin ku zai karu, zaku Sami lada a wurin Allah. Akwai fa'idoji da dama masu amfani akan Haka.  ..... Abinda na hakake a labari shine Jan labari  ba shine ba, matukar sakon da kake son isarwa zai je to a layi biyu ma ya wadatar...... Kadan Mai albarka yafi Mai yawa yuyuyu.
     Rubuta batsa, maganganun banza da rashin kunya ga labari ba shine ke kawo wa mutane kwarjini ga labari ba. Ma'anar labarin , tsabtar sa da Kuma kyautata rubutu saboda Allah. Duk abinda muka rubuta zamuyi depending din sa a wurin Allah. Ya Allah kada ka kamamu da laifin da mukayi bisa ga tunanin munyi da kyakkyawar niyya. Allah ka yafe Mana ka shirya Mana zuri'a.
Qalubale ga itaye, ku daina tura yaran ku makaranta ba tare da binciken abinda sukeyi ba, ku ringa Kai masu ziyarar bazata Kuna saka ido ga yaranku musamman mata, mazan ma abin kula ne Yanzu.
 Yan Mata ku sani bin namiji ka nuna kana sonshi bance haramun bane Amma ku sani kunya ma cikon Imani ce, duk abinda musulunci yazo dashi muna daukarshi da muhimmanci  .
Allah ya sada mu da alkhairi.
  Wanda labarin bai mawa ba sai yayi hakuri.
  Sai mun hadu a wani sabon labarin bayan sallah idan Allah ya kaimu.

*Zainab wowo*πŸ’–
*MAMAN AL'AMYN, AMINATU AND ABDALLAH*


Wa Zai Furta? Page 30 - ZAZZAFA TV




Shiga fejin YouTube namu
Kadanna alamar sunan film din dayake kasan hotonnan domin ku saukeshi akan wayarku ko kuma computerku cikin Sauri da sauki 





0 comments:

Post a Comment