Thursday, July 23, 2020

Wa Zai Furta? Page 27 - Zazzafa TV



23 July 2020

🀐 *WA ZAI FURTA?*🀐
              27

*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri'a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.*


*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*

*Domin ki...... beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*

πŸ‘‰πŸΌπŸ’žπŸ’•πŸ’•  *RUKAYYA  BAKO DAN BATTA I love you so much, remember this always*πŸ₯°πŸ˜πŸ˜˜.

πŸ‘‰πŸΌπŸ’—πŸ’• *Mz na nufin moza ( mother) watau ( Salamatu Dahiru ) wannan page din duka naki ne Allah ya bar mun me MZ ana mugun tare*🀝🏼 ```Aminatu na godiya kina qalbinta```

       **************
*Federal University dutsinma*

   Ya wuntsula ya Mike da sauri keeee kina hauka ne Zaki kifar damu, ki rufa mun asiri Ina son ganin Yan dagwai dagwai.... Ta galla mishi harara sauka munzo... Ya duba da sauri yaga an wangame get, zuwan keda wannan burkin ko kuwa kawon abincin?
   Kinji?
Kazo kaci gidana..... Zaki zo ki daukeni?
In daukeka fa kace, Wai meye amfanin motocin can? Ta nuna da yatsa yayi murmushi kunyar hawan su nake Allah... Ta danyi dariya kunya?
Eh wallahi sai nake ga kamar kowa zai ringa kallona...

 Sai Ni rasa kunya ka sa nake hawan Wagga?
Ya kyalkyace da dariya to ai ku Daman Mata da kyale kyale aka sanku duk neman da mukeyi suwa muke kaiwa kudin? Ko bakiji ance Mana *Bayin Mata muke?*
..... Nidai naji sauka ...kina korata?
A'a Ina dai son naje nayi tuwon ko?
Zaki zo ki daukon please?
Dan Allah Anwar kazo da kanka.... Ya bude motar fine... Zanzo bye take care ya shige .
Tayi Yar dariya kawai ta tafi.
  Karfe takwas yazo shida sadeeq gidan falo biyu ne na farko da na can ciki, bai tsaya komai ba ya wuce ciki abinsa... Sadeeq Kuma ya zauna na farkon shida su Aisha.
 Riga da skirt ne jikinta sun kamata, ta zumbula hijab ta wuce da abincin a tray.
Sai kace muna a gida, ji yanda ka dararrashe... Yayi murmushi kawai.
  Ta zuba mishi komai ta mike.... Ina zakije?
Ke wace irin bagidajiya ce Yar kauye? Haka are serving Mai gida???
Ta galla mishi harara, ya ce, naji dai Amma zauna ki cire wannan hijab din..... Ta zaro ido to Bari na dauko kallabi ko gyale..... Ya ajiye chokali ya kalleta fuska daure.... Ina son ba daddy mamaki Amma da alama wannan gardamar taki zata janyo Miki.... Tayi saurin cire hijab din gashin ta ya warwaro bisa bayanta warrrrrr ya sauka....yabi gashin da kallon ya hadiye tuwo ba shiri Amma duk da Haka bai saki fuska ba....
Ta yi tsumu kunya ta baibayeta, musamman da ta lura Yana yawan kallon kirjinta. Kayan sun matseta duk ta takura.
Ba tare da ya kalleta ba ya ce ```Kinsan kina da kyau Bilkisu?```
Gabanta ya bada ras!
Jin tayi shiru yasa Shi kallon ta yace kinji??
Ta Kara yin shiru....wannan kalmar ta kinji idan ya fada tana Jin kamar ta gantsara mishi cizo....
Bazaki amsa ni ba?
Ya kafa Mata ido, ta danyi murmushi tana Kara sunne kanta sai murza hannu takeyi kamar Mai yin alwala....
Yayi murmushi,kina da kyau Bilkisu Ina son structure dinki ... Tsikar jikinta ta bada wani Yarrrr.....
Ya ajiye chokali tuwon yamun dadi akwai Wanda zakiyi mun dumame da safe?
Um, ta ce a hankali.
Amma kamar generator dinku bashi da karfi ko? Naji AC din Bata tafiya da kyau ko kuwa fault din nata ne?
Huh?? Ya ce Yana kallonta...
Kila, ta fada ahankali... Wai kin takura ne?
A'a ta fada tana sunne Kai.
Bana son wannan ruwan daukon wasu marassa sanyi a can...ya nuna karamin fridge... Ta Mike ya bita da kallo, Koda ta juyo yayi saurin kawar da Kai kamar Yana latsa waya..... Ta mika mishi ya hada da hannun da ruwan ya fizgota , ta fada jikin sa zata kurma ihu ya toshe Mata Baki..... Kina ihu su sadeeq zasuce ga Bilkisu can ana harka...ya fada Yana Yar dariya.
Ta runtse ido jikinta ya Fara kyarma.... Dan Allah kayi hakuri..... Wayyo na shiga uku...
Wannan kunyar taki ke tunzurani kinki sakin jiki dani..... Dan Allah Zan saki sakeni ka gani.... Ya zagayo da hannayen sa ta gaba ya harde su daidai kirjinta ya soko kansa ta wuyanta Yana Mata Rada..... Ke nifa ba dutse bane ko katako.... Ta runtse ido wayyo na shiga uku Dan girman Allah ka sakeni.
  Zan sakeki Amma wallahi Kika motsa kinji na rantse yau ba me kwatarki.... Naji Zan tsaya please na tuba.  .... Ya cire hannuwansa ... Ta saki ajiyar zuciya kanta kasa sai kyarma takeyi duk ta tsorata....
Kyarmar ta mecece ya riko hannunta..... Dan Allah kayi hakuri..ta fada kamar zatayi kuka.... Ya Kara rungumota Dan Allah ki jira....Anwar kace zaka ba daddy mamaki fa.... Eh na sani. Ya fada kasa kasa .
Dan Allah ka sakeni.... Ke wallahi bazan iya ba, Dole na ringa taba ki don ki Saba kunyar Nan tayi yawa....ke Yanzu na say Miki ido kawai ba Dan romance ai Kya ce bani lafiya...... Wayyo ni Bilkisu na shiga uku...ta fada a hargitse .
 Ya shafa gashinta.... Ina son gashinki .... Jikin ta ya bada tsammmmm....ta runtse ido.
Dan Allah kizo muje gidana ki kwana.... Sai kawai ta rushe da kuka.... Ke wasa nakeyi yi shiru.... Ya saketa Yana dariya... Jikinta sai kyarma yakeyi.... Ta goge hawayen ya bita da ido.... Haka kike da tsoro?
Ta hada Kai da guywa kawai....
 Ya Mike shikenan tashi ki saka hijab muje ki rakani ...ya dauko hijab din a hannunsa.
Ta Mike .... Wallahi ko kiyi shiru ko na tafi da ke ... Tayi saurin goge kwallan, yayi murmushi matso na Sanya Miki hijab din... Ta matsa ya rungumota..... Dan Allah ki Dan ban minti biyu .... Ta sunne jikinsa ta Kara sakin kuka.... Ya buga tsoki... Kedai wallahi akwai ruwa ruwa...
 Aure Dadi gareshi ki kwantar da hankalin ki mu.... Ta Kara sunne Kai ..ya kyalkyace da dariya to sakeni shikenan ba abinda zamuyi.
   Ya saketa a hankali, Ya koma ya zauna bisa kujera ya zuki iska ya fesar tare da fadin ohhh my God.
Tayi tsaye har lokacin Bata daina kyarma ba ya fizgota ta fada jikinsa Yana fadin idan Baki saki jiki ba Allah yau sai dai mu kwana anan.... Ta sunne jikinsa, kokarin dagota yakeyi taki yarda.... Yayi dariya to ki daga ni na tashi ko?
 Ta kasa dagowa.....wallahi Zan birkitar dake... Ta Mike da sauri ya riko hannunta tare da mikewa ya janyo bayanta ya kwanto samanta kansa bisa kafadar ta Yana magana cikin Rada Rada.... Bilkisu Ina Jin tsoro fa Anya Zan iya ba daddy mamaki wallahi duk kin rikitani.... Nidai Dan Allah kayi hakuri Anwar na tuba..... To ki jiyo in Baki kiss...... Ta zame ta zukunna tare da kankame jikinta tana fadin wayyo.... Ya Dan zukunna shima.... Wallahi kiss kawai zanyi please....nidai Dan Allah ka rufa man asiri....
Yayi Yar dariya okay naji tashi na tambayeki... Ta Mike da sauri ya matso ta matsa baya... Ya kalleta ya da matsawa?
Ta zumburo baki kayi tambayar inaji.... Ya nufota ta ringa baya baya... Bata Ankara ba taji ta daki bango ta kankame jikinta.... Ya tsaya gabanta ya harde hannuwa ya goya su a kirji tare da kura Mata ido duk sun kankance.....
An taba kissing dinki?
Jikinta ya bata tsammm..... Kinji? Ya fada.
Bazakiyi magana ba?
Wallahi ban taba ba..... Hada wallahi?
Wallahi tallahi ta fada kamar zatayi kuka...
Kina so kiji yanda akeyi?
A'a Dan Allah kayi hakuri.. .... Me yasa bakya so?
Tsikar jikinta ta Kara bada Yarrrr.....kinji?
Hakanan...
Ya sunkuyo daidai fuskarta tare da dafe bangon da hannu yace ki shirya anytime from now Zaki ji yanda akeyi.
Ya tallabota yasa Mata hijab ya figi hannunta suka fito....
Sadeeq shida Aisha kadai a Falon Maryam tayi ciki abinta..... Ta kalleshi idan ka Gama muna waje.....
 Kanta a kasa ta kasa dagowa ta sanyata jikin mota ya matso kusa da ita sosai kamar zasu hada jiki ya Fara Mata magana a hankali.... Ina so ki sani ni ba katako bane,in shaa Allah bazan kasa ba daddy mamaki ba Amma da sharadin sai kin daina wannan kunyar kin sakemun jikinki..... Ta runtse ido ya sunkuya Yana lekenta..... Wannan kunyar taki wallahi tana Sanya mun sha'awar ki Bilkisu tabbas idan Baki saki jiki Dani ba to I have no choice but to sleep with you..... Ta juya ta kife Kai ga mota *na shiga uku ni Bilkisu*..... Ya juyo da ita, matsalar bani da kunya ko a gaban waye Zan iya taba ki don haka kina da aiki ja don duk ranar da na bukaci taba ki Kika Hana kamar yau to ki sani Zan...... Anwar please.... Ta fada tare da runtse ido. Ya kyalkyace da dariya... Sadeeq ne ya fito Shi kadai ba Aisha .... Ya kallesu to pigeon muje ko?
..... Sadeeq yarinyar nan ta fiye kunya fa tana takurani da yawa...
  Tayi sukutiiiii, Sade yayi murmushi Bilkisu ya da kunyar miji Kuma?
Ya zagaya ya shige mota.....Yana fadin kasan baka Gama ba ka fiddoni..?
Ya kalleta sadeeq bai gaji ba ko mu koma?.... A'a kuje Dan Allah...ya Kyalkyace da dariya matsoraciya kizo mun da dumamen school gobe zanci a mota kinji ko?
Ta Dan saki ajiyar zuciya ta ce toh.
Ya langwabar da Kai Bilkisu bana son tafiya wallahi.... Ta ce ya Salam! Amma a zuci...
  Zan say kawo Miki irin pad din kamfanina kiyi amfani da ita ance tana da kyau sosai idan Bata Miki ba Kinga Dole a canza sabuwa..

 Ta mishi banza.
 Yayi murmushi kinji?
Um, ta ce.
Ko Zaki bini..


 Ta ingijeshi ta kwala.  da gudu ya tuntsure da dariya ya fada mota...... Sadeeq anya Zan iya zuba ma yarinyar can ido?
    Ka rufa Mata asiri Dan Allah... Ya fada Yana Yar dariya.
Amma fa tana da tarbiyya sosai could you imagine ta tsorata simply don na yi hugging dinta?
.....wallahi Anwar Bilkisu na bani mamaki ta fita daban daga cikin Mata maganar gaskiya wannan lokacin kafin ka sami yarinya Mai kamun Kai irin ta Yana da wahala kasan abinda ke bani mamaki?
Ya girgiza Kai..
 Yanda she's fully hijabite wallahi kaga fa tun zuwan ta school din nan Bata taba Sanya gyale ba Bata shigar banza ga addini sallah Bata wuce ta cikin jam'i naji ana rade radin ita za a ba Amira.... 
Ya danyi murmushi, wallahi har tausayi ta bani Yanzu duk jikinta ya tsinke da rawa sadeeq ta tsorata da nace zanyi kissing din ta wallahi hada kuka....
Ya kyalkyace da dariya ya ce baiwar Allah.
Sai ka lallaba ta ka Kara daurewa kada ka janyo ma kanka jangwam ta rikice maka Kuma...... Naga alama fa akwai rikici .
Kasan Aisha ta nuna tana da interest akaina?
 Ya kalleshi haba??? 
Ya Dan Bata rai, no Bata mun ba, Ina son mace mai Jan aji nafi so na Sami mace wacce Ni ke binta tana ban wahala ba ita ce zata ringa zakewa ba..... Kamar Bilkisu kenan? Ya katseshi Yana dariya... Yayi murmushi Anya Zan Sami kamar ta at least ma ko wacce bata kaita ba.. da tana da kanwa ko Yar shekara biyar ce Allah da Zan jira..

 Suka kyalkyace da dariya.

    Ya zuki iska ya fesar.... Gaskiya Ina bukatar matata .....ka rufa mata asiri Anwar Dan Allah kaifa da kanka kace zaka bada mamaki...... Kai nifa ba katako bane ko?.
Eh,but at least ka duba yanayin idan ta Sami ciki fa?
Shine me? Ya harareshi, Ina nufin kaga na farko tun a laulayi idan Mai Shan wahala ce an Sami matsala musamman ga karatunta, kaga automatic spill over, na biyu bazata taba fita zargin mahaifan ta ba cewar ita ta sanar da Kai akwai Aure bayan an gargadeta da tayi shiru,na uku karatu da goyo Anwar is not easy akalla.... enough jor.... Ya daga mishi hannu... Amma Zan ringa Dan romancing dinta gaskiya ban iya daurewa..... Romance din zai ringa Sanya maka sha'awa akwai ranar da wallahi zaka kasa controlling kanka  tunda kamar yanda ka fada din Kai ba katako bane...... Ya Allah !!! ya fada tare da maida Kai ya kwantar bisa sit, sadeeq meye dabara?
  Ina ga mu rage ziyarar su gida , ka ringa tsareta school duk maganar da zakuyi nasan idan kana ganin jama'a bama zaka kawo komai a ranka ba..... Nawaoooo,!!! Ya fada tare da tashi zaune.. gaskiya nidai an kwareni ....
 Sadeeq ya kyalkyace da dariya rawar kanka ta janyo maka....... Ya Kai mishi duka, naje nayi. 
  Yanzu dai ai daga wannan semester din saura daya ko?
  Biyu dai....
 Ya katseshi ...ya ja dogon tsoki kawai ya kwanta tare da runtse ido. Sadeeq ya bishi da kallo Yana murmushi......
Wai ya mufeeda ta hakura ko?
Ya yatsuna fuska, ance har yau ta kasa shigowa school saboda kunya..... Maganin ta kenan... Ya tashi zaune Yana Yar dariya kasan ni duk wake bani dariya?
Ya ce sai ka fada.
Helen, tunda akayi case din nan Yanzu ko layin da nake zaune Bata bi kasan arna da shegen tsoro....... Suka kyalkyace da dariya.

     Bilkisu ta zabga uban tagumi har lokacin jikin ta bai daina rawa ba, kirjinta kuwa sai dakan uku uku yakeyi, *Na shiga uku ni Bilkisu Wai kiss* .... Nikam dama na hakura da Abujan da Yanzu Ina can zamana qalau..
   Ta runtse ido lokacin data tuna ya zagayo da hannayen sa bisa kirjinta ya kwanto jikin ta...... Tsikar jikinta tashi Yarrrr lallai akwai damuwa .... Ta bude ido su maza basa da kunya ko kadan....
Haka ta kwanta tana ta juye juye da ta tuno Shi da yanda ya ringa Mata sai ta kudundune jikinta ta boye kanta cikin filo.....
  Murjanatu cikin masu aikin gidan ta Kira da sauri ta ce maza ta dumama tuwon jiyan kafin ta fito wanka.....
   Yau taga amfanin nikaf, saboda da Babu ita tasan bazata iya kallon Anwar ba.....
   Tana shiga ajin anata raba test din da Richard munafuki yayi. Two over ten, three mutum biyu keda 5 su chinayye...... Itama two taci, Anwar ya saka tashi aljihu kawai lokacin da ya buda yaga yaci nine....
Ya kame Baki na shiga uku.... Mutumen nan wallahi mugu ne daman yafi so mu fadi.... Sadeeq na bayanta ya ce nawa Kika ci Bilkisu?
Ta mika mishi 2 ce shegen kaifa? Yayi murmushi three..... Anwar yayi fit ya fizge takardar ya na zagayo ya kalli root dake kusa da ita yace ban wuri.... Ta kwashi takardun ta ta koma sit din da ya taso.... Basai ka fizge ba two ce kai nasan nine kaci don ma baya bada cikon da tabbas ten zaka ci....... Inji waye ya fada Yana murmushi....ta zumburo Baki nidai fiddo naga Ni...... Ya Mika Mata Yana murmushi.... Kamar jira ake taje hannun Bilkisu aka Fara rokonta ta bada ayi snapping.... Ta Mika musu.
  Mutumen can na daga mun hankali bana kaunar Dan iska.... Yayi dariya Kuma duk da Haka Baki taba faduwa course dinsa ba ko?
Ta harareshi Amma da yake akwai nikaf bai gani ba tace da hawan jini, da na ruwa  ko?,ya kyalkyace da dariya, toh eh Mana,duk sai ya gama tayar Mana da hankali tukun Kuma *E* din nan dai ce ko *D* ..... Ina laifi ai yafi carry over ko?...... Zatayi magana malamin ya shigo..... Ya fiddo waya ya dan Mata magana a hankali..... Shiga WhatsApp...
```kinyi barci jiya?```

Ta maida mishi da ```me zai hana?```

```ni kuwa kasawa nayi saboda tunanin ki```
Ta kasa cewa komai

```kinji```
Ta ce ```Hmmm```

  ```smiles kin zo mun da tuwon?```

```yana mota```

```ina zamuje naci```?
  
```ina fa, anan waje ko?```

```Bana son waje is too open let's go to the field or new lecture rooms side I need quite place okay?```

Tayi shiru.

``` kinji ko?```

Ta maida hankali gun lecture.... Ya zunguro ta da hannu ....dole ta rubuta mishi

```naji```

Yayi murmushi.

``` sai Anja mun aji?```

```Ka bar mu muji lecture Anwar```

.....```ke ni ban wani ganewa ki Bari kawai zamuyi tutorial```

```Hmmm``` 
Malamin na lura dasu,
Yana gamawa ya ce tear a sheet of paper write your number only......

*Mun shiga uku ka ga abinda nake gudu ko?*
Ya sumke Yana Mata dariya.

Kina da black biro?.....
Banda Shi ta fada cikin tsiwa.
To kiyi sauri ki wanka ko na rubuta miki,?
Kawai kayi na kwafa idan Kuma ya tayar Dani shikenan.....
Yayi murmushi....
Ya Fara dictating questions based on what he discussed.
  Ta Kara tsure Mata tana magana kasa kasa ... Wallahi kana ja mun wannan semester din..... Yayi shiru Yana murmushi Yana rubutu.
  Tana kokarin Jan layi ya turo Mata takarda har ya Gama Daman two questions ne. Ya ci gaba da rubuta nashi Yana layin karshe kawai malamin ya ce hands up...... Amma sai da ya karasa Kai Anwar karshe ne......ta galla mishi harara cewa zakayi kasan abinda ka taka, yayi dariya to meye acikin nan cubweb theory din ke da wahala?

Ta ce hmm, duk ya Gama birgeta, gunguni kawai ke tashi cikin ajin.
Yana zuwa layin ya karba ya dan harari Anwar din ya wuce ....
Yana fita sadeeq ya taso kaga mutumen Nan ko?
Yayi murmushi bana fada ma ba, gaskiya naji dadin bayanin jiya... Ta kalleshi da sauri au Daman kunyi wannan din?
Sadeeq ya ce wallahi jiya kamar wasa ya koyan Kinga da yau naci kaniya ta...... Ta ce hmmm kawai,
Anwar ya kalleta kema yau zamu Fara karatu kiyi hakuri..... Na fito karfe hudu kenan?
A'a ki Bari sai after Isha zanzo gidan....
Gabanta ya Fadi, na marecen nake ga zaifi ko kuwa?
No!, Bana son yawan fita inba lecture akeyi ba, kawai ki jira zanzo kinji ko?
Toh, ta ce a hankali.
Ya Mike muje....
    Ka Kira sadeeq muje yaci..... Zan rage mishi ..
Anwar meye Haka? Wasa tare ci banban.... Ya danyi dariya yarinya kawai kice kina son wani kusa kada muje na cinyeki Ni kadai.... Laaaa ni ba Haka nake nufi ba..... Sadeeq!!! Ya kwala mishi Kira....
Ya karaso Yana murmushi ya akayi?
Tuwo aka kawon Wai bazan ci ni kadai ba sai tare da Kai... Yawwa Bilkisu Allah dai ya biya kin San kuwa yunwa nakeji wallahi.... Ya banka mishi harara Kuma Kai baka wuce tayi ko?
  Ban wucewa kin ganshi Nan ko ruwan zafi bai iya dafawa .... Duk suka kwashe da dariya.
Ina zamuci tuwon?
Field... Anwar ya bashi amsa.
Okay kuyi gaba Zan biyo ku da mashin.
Ungo nidai kaja motar Dan Allah..... Ya wurga mata harara ya fada gaba ya zauna kawai.
Dole ta shiga ta ja motar a hankali.... Duk inda suka gitta sai an bisu da kallo.. ba karamin kashe zuciyoyi sukeyi ba a school din suna bada *Plus*
   Sadeeq na gama ci yabar wurin yace zaije aski.
  ....me Zaki dafa mun da dare?
 Abinda kake so, ta fada..... Ke daga nikaf din nan na ringa ganin idonki.... Ya karasa maganar Yana yakice Shi .... Ta yi kasa da Kai tana murmushi..... Ya shafa gefen fuskar ta Yana fadin ```lemme see this baby face``` ... Ta to dariya ta ce kaiiiiiii.....
  Yes, ya fada Yana Kara kallonta,
Me Zaki dafan?
Abinda kake so, ta Kara maimaitawa.
Kiyi mun chips mana.
Toh, ta fada a hankali.
Babban fridge din nan Kinga akwai kaji da naman rago da kawuna ko?
Um, ta ce.
Idan kina bukatar kifi kiyi mun magana a kawo Miki Shi kinsan baya da dadin ajiya saboda karni ko?
  Gaskiya fa.
Me yasa baki taba rokona wani Abu ba? 
Ta kyalkyace da dariya kaiii Anwar... Yabi fuskar da kallo..... Yana murmushi.
```Bilkisu kin San cewa ke din ta daban ce kuwa?```
Na sani Mana... Ta fada tana murmushi.
Ya akayi kika sani.....
Tayi dariya saboda *Bushara na Sona*..... Ya kyalkyace da dariya for the first time kin kirani *Bushara* Dole na Miki kyauta yau Zan canza Miki motar Nan...... Dan Allah ka barta Ina sonta....... Karki damu ai ba rokona kikai ba, Ina son ki bar tarihi FUDMA a ringa kwatancen mu..
.. Yanzu ma anayi.
In tambayeki???
Ta ce um,
Yaushe Kika Fara Jin kina Sona?
Ta yi kasa da Kai tana dariya.....
Kunya kike ji?
Ta Kara murmusawa..... Okay rubuta mun ta WhatsApp..... Ka Bari Zan fada maka..... Yaushe?.
Tayi shiru tana murmushi.
Kunyar ki tayi yawa Bilkisu.... 
Muje ki ajiyeni gida .
Ta tayar da mota, 
Har ciki ta shiga yau, ya ki fita ya tsareta da ido sai kuma ya ce affff.... Ki jirani Ina zuwa please ya shiga gidan da gudu.....
Ta bishi da kallo tare da sakin ajiyar zuciya a hankali....
Ya dawo dauke da Yar leda Mai kyau a hannunsa, ya leko ta taga, it might be Baki zo da English wears ba ko?
Kisa wannan anjima.... Ta zaro ido... 
Ya Kara sunkuyawa ba abinda Zan Miki Allah kuwa kawai Ina son ganinki cikin su matsala daya za a Samu idan kika Fara wannan kunyar taki lallai Zaki janyo ma kanki na taba ki.... Ban Baki a boye ba, just wear it and feel free okay????
Ta daga Kai a hankali.... Yayi murmushi that's my babe...... Tayi baya da motar ta fita a hankali duk jikinta yayi sanyi duk da bata ga kalar kayan ba.....
  Yabi motar Yana murmushi... Ya ce tsoron ta yayi yawa gaskiya. Ya zuki iska ya fesar ya wuce ciki.
  Ta zabga uban tagumi daki ita kadai ta zuba ma kayan ido, doguwar riga ce Mai kame jiki da hannun vest, daga kasa akwai     tsaga har kusan guywa maroon ce Dana da wani katon belt bisa kugu, da jefi jefin flowers jikin rigar red.    Aisha ta taimaka Mata sukayi farfesun kaji, sannan suka soya chips din kaskon karshe ta shiga tayo wanka tabar Aisha ta karasa ta feshe jikin ta da turaruka masu kamshi ta gyara gashinta Amma ta mishi gammo ta nade tare da zumbula katuwar hijab.... Tana fitowa taci karo da Aisha bakin kofa zata shigo ....Wai duk meye kikeyi haka ga Anwar can yazo.... Gabanta ya bada ras!.... Shida sadeeq ne?
A'a Shi kadai ne gaskiya... Kin saka ma coconut juice din ice ?
Eh Yana fridge muje na Kama Miki.... Barshi baya son haka, ta katse ta.
Yana zaune kasa ya Mike kafa Yana ta latsa waya sanye da farin boyel Mai laushi kansa ba hula.
Ta ajiye plate din chips din da cooler farfesun ta ce ... Ina wuni?
Ya Dan dago sai Shan kamshi yakeyi ya ce ... Bilkisu ya kike?... Na Sanya ki aiki ko?
Ba komi, ta fada tare da mikewa... Ya bita da kallo duk kamshin turarenta ya kashe Masa jiki.
  Ta dawo da sauran kayan ta zuzzuba mishi Yana satar kallonta da wutsiyar ido, da tazo dagowa sai ya basar.
  Tana gamawa ya tura Mata Wanda ta zuba mishi ya janyo sauran da ke cooler gaban Shi ya ce wallahi sai kin cinye duka Koda zakiyi amai.... Ta dago Kai da sauri ,.. ya hade girar sama da kasa yasha mur ...
  Dole ta dage ta Fara ci sai da tafi Rabi yaga da gaske turawa takeyi sannan ya ce mikon dankalin na Kara bai isheni ba.... Ta tura mishi da sauri ya cinye... PeppΓ© soup din Nan  yayi dadi fa.
Jeki Kai kayan kizo da books din da zamuyi ba dadewa zanyi ba.....
Ta mike da sauri ya bita da kallo sai kawai yayi dariya.... Tana dawowa ya Kara hade fuska.... Kina jira na ce ki cire hijab din????
A hankali tayi sama da ita.... Tsikar jikinsa ta bada Yarrrr, ya hadiye wani tsinkakken miyau sai kawai yayi kasa da Kai ya Fara budo littafin da ta Miko....
Tunda ya Fara bayani bai dago ba ..... Tun tana Jin kunya da tsoro har ta fahimci Sam ba ta ita yake ba gashi sai wani Shan mur yakeyi.....
Tana ganewa sama sama har sukayi course biyu.
Duk ta makure... Ya dago Kai kina ganewa kuwa?
Um, ta ce da sauri, saura kadan yayi dariya.
   Yau barci nayi da Rana sosai...
Wai kin San cewa an gano nine Bushara school din Nan?
Ta danyi murmushi, nasan za a gane Kam...
Saboda me Kika ce haka?
To Anwar ko wadannan kattin da ke Bina da wadanda ke gidanka yaci asan Kai waye.... Ya danyi dariya inji waye kawai tsabar sa ido ne.
  Naji class din mu za a yi jacket da shirt na graduation Ina ga ni Zan dauki dawainiya ko?
Ya dai kamata. Ta fada kanta kasa.
Yayi murmushi, Nima Ina son yiwa yaran Nan alheri me kike ga Zan raba musu?
Kudi, ta fada.
Kudi Kuma?
Eh, Mana kudi zaifi saboda kowa yasan meye damuwan sa Kuma kudi ke maganin komai ko kuwa?
Kuma fa, Shi yasa nake sonki wallahi saboda kina da hankali...kamar nawa Zan basu?
Yanda kayi niyya Kuma ai kafi kowa sanin iya karfin ka.
  Ya kura Mata ido, ki fada mun Mana ai Yanzu shawara mukeyi nida ke ko?
  Ka dai kiyasta Ni ban San nawa zance ba ko kayi shawara da sadeeq..... Da ke zanyi. Nawa kike ga ya Dace na raba masu?.
Tayi shiru... Ka Bari zanyi tunani toh.
Okay, sai na jiki tashi ki karon ruwan in Sha... Ta Mike ya bita da ido, kafin tazo kawai ya Mike kamar Mai neman wani abu, 
Tana kokarin Miko mishi ya mameta ya kamo sai kawai taji ya hada bakin sa da nata, ta saki ruwan kasa..........✍πŸΌπŸ˜„πŸ™ˆ

*Zainab wowo mamar Abdallah*πŸ’–

*Mz , mz, mz Ina nufin ( salamatu Dahiru ) Allah ya Kara zumunci mother kina Raina koda yaushe.*


*ALLAH YABARKI DA ALHAJI NURA NA'IMA AMADU SPEAKER YAN ADAWA BAKU IYAWA MUNE AMARYA KUMA UWARGIDA MUTU KA RABA IN SHAA ALLAH*πŸ’žπŸ’žπŸ’ž



*Yauma page daya za'a samu Ina busy*


Wa Zai Furta? Page 27 - Zazzafa TV




Shiga fejin YouTube namu
Kadanna alamar sunan film din dayake kasan hotonnan domin ku saukeshi akan wayarku ko kuma computerku cikin Sauri da sauki 





0 comments:

Post a Comment